2 Tas 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi mana addu'a, Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗuwa, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku,

2. a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba.

3. Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan.

4. Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi.

5. Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.

2 Tas 3