15. Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al'amari ba, ko a kan sha'anin taskoki.
16. Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.
17. Sai Sulemanu ya tafi Eziyon-geber da Elat da suke a gaɓar teku a ƙasar Edom.
18. Hiram kuwa ya aika wa Sulemanu jiragen ruwa tare da barori waɗanda suka saba da sha'ani a teku. Sai barorin tare da barorin Sulemanu, suka tafi Ofir, suka ɗauko zinariya talanti ɗari huɗu da hamsin, suka kawo wa sarki Sulemanu.