2 Tar 7:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sa'an nan Sulemanu ya tsarkake tsakiyar filin da yake a gaban Haikalin Ubangiji, gama a wurin ne ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayu domin salama, saboda bagaden tagulla wanda Sulemanu ya yi bai iya ɗaukar hadayu domin ƙonawa, da ta gari, da ta kitse ba.

8. A wannan lokaci, Sulemanu ya yi biki a wurin har kwana bakwai, tare da dukan Isra'ilawa, da waɗanda suka zo tun daga ƙofar Hamat, har zuwa rafin Masar, taron kuwa mai girma ne ƙwarai.

9. A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.

10. A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama'a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama'arsa Isra'ila.

11. Haka kuwa Sulemanu ya gama Haikalin Ubangiji da fādar sarki. Ya fa yi nasara cikin dukan irin abin da ya yi niyya game da Haikalin Ubangiji da fādarsa.

12. Sa'an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu'arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya.

13. Har idan na kulle sammai yadda ba za a yi ruwan sama ba, ko kuma in umarci fara su cinye ƙasar, ko kuwa in aiko da annoba cikin jama'ata,

14. in jama'ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali'u, su yi addu'a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa'an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.

15. Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu'ar da za a yi a wannan wuri.

16. Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.

2 Tar 7