2 Tar 7:21-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. “Haikali kuwa, wanda aka ɗaukaka, duk mai wucewa zai yi mamaki ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa wannan ƙasa da wannan Haikali haka?’

22. “Sa'an nan kuma za su ce, ‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala'i.’ ”

2 Tar 7