1. Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima.
2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al'ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama'ar Isra'ila suke yi.
3. Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.
4. Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.”
5. Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji.