6. Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim.
7. Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye.
8. Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida.
9. Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya tsantsa.
10. Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya.
11. Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.