2 Tar 3:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse.

2. Ya fara ginin a ran biyu ga watan biyu a shekara ta huɗu ta sarautarsa.

3. Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin.

2 Tar 3