6. Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al'amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.
7. Sauran ayyukan Yotam, da dukan yaƙe-yaƙensa da al'amuransa, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza.
8. Ya ci sarauta, yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima.
9. Sai Yotam ya rasu, suka binne shi a birnin Dawuda. Ahaz ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.