Allah ya ƙaddara hallakar Ahaziya ta zo ta wurin ziyarar da ya kai wa Yehoram. Gama sa'ad da ya zo, sai ya fita tare da Yehoram don su yi yaƙi da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya keɓe don ya kakkaɓe gidan Ahab.