2 Tar 22:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.

2. Ahaziya yana da shekara arba'in da biyu sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri.

3. Ya kuma bi gurbin gidan Ahab, gama tsohuwarsa ita ce mai ba shi shawarar yadda zai aikata mugunta.

4. Ya kuwa aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar gidan Ahab, gama su ne mashawartansa bayan rasuwar tsohonsa, wato shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

5. Ya kuwa bi shawararsu. Ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab, Sarkin Isra'ila, don su yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya, a Ramot-gileyad. Suriyawa kuwa suka yi wa Yehoram rauni.

2 Tar 22