2 Tar 20:19-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai Lawiyawa daga Kohatawa da Koratiyawa suka tashi tsaye suka yabi Ubangiji Allah na Isra'ila da babbar murya.

20. Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”

21. Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce,“Ku yi godiya ga Ubangiji,Saboda madawwamiyar ƙaunarsaTabbatacciya ce har abada.”

22. Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su.

2 Tar 20