2 Tar 16:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.

6. Sa'an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba'asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.

7. A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.

8. Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka.

9. Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko'ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al'amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”

2 Tar 16