2 Tar 12:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da mulkin Rehobowam ya kahu, ya kuma yi ƙarfi, sai Rehobowam da dukan Isra'ilawa tare da shi suka bar bin shari'ar Ubangiji.

2. A shekara ta biyar ta mulkin sarki Rehobowam, Isra'ilawa ba su bi Ubangiji da aminci ba, saboda haka Shishak, Sarkin Masar, ya hauro don ya yi yaƙi da Urushalima.

3. Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa.

4. Ya ci birane masu kagara na Yahuza, har ya dangana da Urushalima.

2 Tar 12