2 Tar 11:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki.

2. Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce,

3. “Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra'ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce,

4. ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da 'yan'uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al'amari daga gare ni yake.’ ” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.

5. Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza.

6. Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa,

7. da Bet-zur, da Soko, da Adullam,

2 Tar 11