Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki.