1. A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.
2. Aka kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya.
3. A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar.