A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.