Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”