2 Sar 22:19-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.

20. Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ”Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.

2 Sar 22