2 Sar 21:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.”

5. Ya gina wa taurarin sama bagadai a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji.

6. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

7. Siffar gunkiyan nan Ashtoret wadda ya yi, ya kafa ta a Haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Sulemanu, “A cikin wannan Haikali a Urushalima wadda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila zan tabbatar da sunana har abada.

2 Sar 21