2 Sar 21:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Amma mutanen ƙasar suka kashe waɗannan da suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar. Sai suka naɗa Yosiya ɗan sarki, ya gāji tsohonsa.

25. Sauran ayyukan da Amon ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

26. Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.

2 Sar 21