Sa'an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye.