1. Sa'ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal.
2. Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.
3. Akwai wata ƙungiyar annabawa da take a Betel suka zo, suka ce wa Elisha, “Ko ka sani, yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”Elisha ya ce, “I, na sani, amma mu bar zancen tukuna.”