24. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
25. Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.
26. Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
27. A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin.
28. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
29. A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.
30. Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa'an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya.
31. Sauran ayyukan Feka da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
32. A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
33. Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, 'yar Zadok.
34. Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi.
35. Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.
36. Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
37. A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza.
38. Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.