1. A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
2. Yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima.
3. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi.
4. Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai.
5. Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.