9. Amma Dawuda ya ce wa Rekab da Ba'ana, 'ya'yan Rimmon, mutumin Biyerot, “Na rantse da Ubangiji wanda ya fanshe ni daga kowace masifa,
10. sa'ad da wani ya kawo mini labari cewa, ‘Saul ya mutu,’ mutumin ya yi tsammani albishir ne ya kawo mini, sai na kama shi na kashe shi a Ziklag. Ladan da na ba shi ke nan saboda labarinsa.
11. Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?”