Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.