2 Sam 22:22-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Gama na kiyaye dokar Ubangiji,Ban yi wa Allahna tayarwa ba.

23. Na kiyaye dukan dokokinsa,Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.

24. Ya sani ni marar laifi ne,Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.

25. Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina,Gama ya sani ba ni da laifi.

26. “Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci,Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.

27. Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka,Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.

28. Kakan ceci masu tawali'u,Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.

29. “Ya Ubangiji, kai ne haskena,Kana haskaka duhuna.

30. Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana,Da iko domin in murƙushe tsaronsu.

2 Sam 22