2 Sam 18:30-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.

31. Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”

32. Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?”Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”

33. Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”

2 Sam 18