Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan 'ya'yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.