Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa'ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”