1. Bayan rasuwar Saul, sa'ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag.
2. Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.
3. Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”
4. Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5. Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”