1. Wato, har ila yau, yabon kanmu za mu fara yi kuma? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi?
2. Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă san ta, ya kuma karanta ta.