2 Kor 10:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.

4. Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.

5. Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.

6. A shirye muke kuma mu hori kowane marar biyayya, muddin biyayyarku ta tabbata.

7. Ku dubi abin da yake bayyane mana! in dai wani ya amince na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda yake shi na Almasihu ne, mu ma haka muke.

2 Kor 10