2 Kor 10:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,

2. ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne.

3. Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.

4. Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.

2 Kor 10