10. da Yuz, da Sakiya, da Mirma. Waɗannan su ne 'ya'yansa maza, shugabannin gidajen kakanninsu.
11. Hushim kuma ta haifa masa waɗansu 'ya'ya maza, su ne Abitub da Elfayal.
12. 'Ya'yan Elfayal, su ne Eber, da Misham, da Shemed wanda ya gina Ono da Lod da ƙauyukansu, da
13. Beriya, da Shimai, su ne shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Ayalon waɗanda suka kori mazaunan Gat,
14. da Ahiyo, da Shashak, da Yeremot.
15. Zabadiya, da Arad, da Eder,
16. da Maikel, da Ishfa, da Yoha, su ne 'ya'yan Beriya, maza.
17. Zabadiya, da Meshullam, da Hizki, da Eber,
18. da Ishmerai, da Izliya, da Yobab, su ne zuriyar Elfayal.
19. Zuriyar Shimai, su ne Yakim, da Zikri, da Zabdi,
20. da Eliyenai, da Zilletai, da Eliyel,
21. da Adaya, da Beraiya, da Shimrat.
22. Zuriyar Shashak, su ne Isfan, da Eber, da Eliyel,
23. da Abdon, da Zikri, da Hanan,
24. da Hananiya, da Elam, da Antotiya,
25. da Ifediya, da Feniyel.
26. Zuriyar Yeroham, su ne Shemsherai, da Shehariya, da Ataliya,
27. da Yawareshiya, da Eliya, da Zikri.
28. Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakanninsu a zamaninsu, waɗanda suka zauna a Urushalima.
29. Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a can. Sunan matarsa Ma'aka.