1. Ra'ubainu shi ne ɗan farin Isra'ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba 'ya'yan Yusufu, maza, ɗan Isra'ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba.
2. Ko da yake Yahuza ya rinjayi 'yan'uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.
3. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, wato ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
4. 'Ya'yan Yowel, maza, su ne Shemaiya, da Gog, da Shimai,
5. da Mika, da Rewaiya, da Ba'al,
6. da Biyera wanda Tiglat-filesar Sarkin Assuriya ya kai bauta. Shi ne shugaban Ra'ubainawa.
7. Danginsa bisa ga iyalansu da asalinsu a zamaninsu, su ne sarki Yehiyel, da Zakariya,
8. da Bela ɗan Azaz, wato jīkan Shema, ɗan Yowel, wanda ya zauna a Arower har zuwa Nebo da Ba'al-meyon.