1 Tar 27:16-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ga jerin sunayen masu mulkin kabilan Isra'ila. Ra'ubainu: Eliyezer ɗan Zikri, Saminu: Shefatiya ɗan Ma'aka, Lawi: Hashabiya ɗan Kemuwel, Haruna: Zadok, Yahuza: Eliyab ɗaya daga cikin 'yan'uwan sarki Dawuda, Issaka: Omri ɗan Maikel, Zabaluna: Ishmaiya ɗan Obadiya, Naftali: Yerimot ɗan Azriyel, Ifraimu: Hosheya ɗan Azaziya, Manassa ta Yamma: Yowel ɗan Fedaiya, Manassa ta Gabas: Iddo ɗan Zakariya, Biliyaminu: Yawasiyel ɗan Abner, Dan: Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabannin kabilai.

1 Tar 27

1 Tar 27:1-34