1 Tar 23:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.

19. 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.

20. 'Ya'yan Uzziyel, maza, su ne Mika, da Isshiya.

21. 'Ya'yan Merari, su ne Mali da Mushi. 'Ya'yan Mali su ne Ele'azara da Kish.

22. Ele'azara kuwa ya rasu ba shi da 'ya'ya maza, sai 'yan mata kaɗai, sai 'yan'uwansu, 'ya'yan Kish, maza, suka aure su.

23. 'Ya'yan Mushi, maza, su uku ne, wato Mali, da Eder, da Yerimot.

1 Tar 23