Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama'arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra'ila?”