Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.