1 Tar 20:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra'ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.

6. Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.

7. Sa'ad da ya yi wa mutanen Isra'ila ba'a, sai Jonatan ɗan Shimeya, wato ɗan'uwan Dawuda, ya kashe shi.

8. Waɗannan uku ne Dawuda da jama'arsa suka kashe daga zuriyar ƙattin na Gat.

1 Tar 20