1 Tar 2:35-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Sai Sheshan ya aurar wa Yarha baransa da 'yarsa, ita kuwa ta haifar masa Attai.

36. Attai shi ne mahaifin Natan, Natan kuma shi ne mahaifin Zabad.

37. Zabad kuwa shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne ya haifi Obida.

38. Obida shi ne mahaifin Yehu, Yehu kuma shi ne mahaifin Azariya.

39. Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa.

40. Eleyasa shi ne mahaifin Sisamai, Sisamai shi ne mahaifin Shallum.

41. Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya shi ne mahaifin Elishama.

42. Ɗan Kalibu, ɗan'uwan Yerameyel, shi ne Mesha ɗan farinsa wanda ya haifi Zif. Zif ya haifi Maresha wanda ya haifi Hebron.

43. 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Kora, da Taffuwa, da Rekem, da Shema.

44. Shema shi ne mahaifin Raham wanda ya kafa Yorkeyam. Rekem kuwa shi ne mahaifin Shammai.

45. Shammai shi ne mahaifin Mayon, Mayon kuwa shi ne mahaifin Bet-zur.

46. Efra ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Haran, da Moza, da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.

47. 'Ya'yan Yadai, maza, su ne Regem, da Yotam, da Geshan, da Felet, da Efa, da Sha'af.

1 Tar 2