1. Sa'ad da Dawuda yake zaune a fādarsa, sai ya ce, wa annabi Natan, “Ga shi, ni ina zaune a cikin gidan da aka yi da itacen al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana cikin alfarwa.”
2. Natan ya amsa masa ya ce, “Ka yi duk abin da zuciyarka ta ɗauka, gama Allah yana tare da kai.”
3. Amma a wannan dare Ubangiji ya yi magana da Natan, ya ce,
4. “Ka tafi, ka faɗa wa bawana, Dawuda, cewa ni Ubangiji na ce, ‘Ba za ka gina mini ɗakin da zan zauna a ciki ba.
5. Gama tun ranar da na fito da Isra'ilawa ban taɓa zama a cikin ɗaki ba, amma daga alfarwa zuwa alfarwa, daga wannan mazauni kuma zuwa wancan.
6. A dukan wuraren da na tafi tare da Isra'ilawa, ban taɓa faɗa wa wani daga cikin hakiman Isra'ila, waɗanda na ba da umarni su yi kiwon jama'ata, cewa su gina mini ɗaki da itacen al'ul ba.’
7. “Saboda haka fa sai ka faɗa wa bawana Dawuda cewa, ‘Ni Ubangiji Mai Runduna, na ɗauko ka daga kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila.
8. Na kuwa kasance tare da kai a duk inda ka tafi, na kuma hallaka maƙiyanka a gabanka. Zan sa ka shahara kamar waɗanda suka shahara a duniya.
9. Zan zaɓo wa jama'ata, wato Isra'ila, wuri, zan dasa su, su zauna a wuri na kansu, don kada a sāke damunsu, kada kuma masu mugunta su ƙara lalata su kamar dā,
10. tun lokacin da na sa hakimai su shugabanci jama'ata Isra'ila. Zan rinjayi dukan maƙiyanka. Banda wannan kuma na yi alkawari zan ci dukan maƙiyanka, in mallakar da su ga zuriyarka.
11. Sa'ad da lokacinka ya yi da za ka mutu, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarka, ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza, zan kafa mulkinsa.
12. Shi ne zai gina mini Haikali, zan kafa gadon sarautarsa har abada.