1. Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al'ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda.
2. Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya tabbatar masa da sarautar Isra'ila, mulkinsa kuwa ya ɗaukaka ƙwarai saboda jama'arsa, Isra'ila.
3. Dawuda kuwa ya ƙara auren waɗansu mata a Urushalima, suka haifi 'ya'ya mata da maza.
4. Ga sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,