1 Tar 14:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al'ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda.

2. Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya tabbatar masa da sarautar Isra'ila, mulkinsa kuwa ya ɗaukaka ƙwarai saboda jama'arsa, Isra'ila.

1 Tar 14