1 Tar 10:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai suka ajiye kayan yaƙin Saul a gidan gumakansu, suka kuma rataye kansa a gidan gunkin nan, wato Dagon.

11. Sa'ad da mutanen Yabesh-gileyad suka ji irin abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12. sai dukan ƙarfafan mutanensu suka tafi suka ɗauki gawar Saul, da gawawwakin 'ya'yansa, suka kawo a Yabesh suka binne ƙasusuwansu a ƙarƙashin itacen oak cikin Yabesh. Suka yi azumi har kwana bakwai.

13. Haka nan Saul ya mutu saboda laifin da ya yi wa Ubangiji, gama bai kiyaye maganar Ubangiji ba, saboda kuma ya nemi shawara wurin masu mabiya.

14. Amma bai nemi Ubangiji ba. Domin haka Ubangiji ya kashe shi, ya ɗauki sarautar, ya ba Dawuda ɗan Yesse.

1 Tar 10