1 Sar 7:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.

2. Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al'ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al'ul a bisa ginshiƙan.

1 Sar 7