1 Sar 6:36-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al'ul.

37. A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib.

38. A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.

1 Sar 6