1 Sar 6:24-25-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne.

4. Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje.

5. Ya kuma gina bene mai ɗakuna a jikin bangon Haikalin daga gefe, da kuma bayan Haikalin, har hawa uku, kowanne kamu bakwai da rabi.

6. Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.

7. An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa'ad da ake ginin Haikalin.

8. Ƙofar domin ɗakuna na ƙasa tana wajen dama na Haikalin. Akwai matakai zuwa hawa na tsakiya da zuwa bene na uku.

9. Ta haka ya gina Haikalin, ya rufe shi da katakan itacen al'ul.

24-25. Dukan kerubobin irinsu ɗaya girmansu kuma ɗaya. Tsawon kowane fiffike na kerub ɗin kamu biyar, wato tsawon daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan fiffike kamu goma ne.

26. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.

27. Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.

28. Ya dalaye kerubobin da zinariya.

29. Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.

30. Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.

31. Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka.

32. Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa'an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.

33. Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun.

34. Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir,

1 Sar 6